
YADDA AKE AMFANI DA INDICTORS
Idan har Ana magana akan TRADING Indicators a cikin Kasuwa, yadda abun yake da ban da yadda wasu mutanen suke kallon shi, ko suke fahimtar shi!...
Yadda ake amfani da indicators wajan gane shiga ko fita daga kasuwa yana da kyau.
ko wacce Indicator akwai Yana yin da ake duba wa na kasuwa kafin ayi Amfani da ita wajan neman Entry ko Exit:
Mu ɗauki misali da Bollinger band (BB):
BOLLINGER Lagging indicator ce, da take bamu labarin abu a kasuwa da zarar ya faru.
Kamar Misali da zarar anyi Breakout na wani support ko resistance a cikin kasuwa. A lokacin da muka ga an fasa Upper Band na wannan BB ɗin zai tabbatar mana da cewa ba anyi successful Breakout (Duk da yakan iya zama Fakeout' shima) Amman dai yana wuya ba kamar a Price action ba.
Da muka yi Magana akan "Lagging indicator", sannan kuma mukace BB tana ɗaya daga cikin irin waɗannan categories na Lagging indicator.
Ina nufin cewa ita ɗin Indicator ce da take bayyana mana abu da zarar ya faru, kamar yadda nayi misali a sama.
Domin fahimtar Lagging indicators sosai da bari muyi misali da abun yake faruwa a zahiri, wanda yake nuni da Alama (Indicator).
Misali: idan kaga hayaƙi ya taso daga sama, kaga wannan yana nuna maka cewa wuta ta kama a wannan wajan da hayaƙin yake tasowa, kaga ai babu yadda za'yi muga hayaƙi a sama wuta bata kama ba, Dole idan muka ga hayaƙi na tashi hakan indicator ne dake bamu labarin wuta ta ta kama.(Irin wannan sune ake kira da Lagging).
Amman a misalin RSI Dana bayar(A rubutun da nayi dazu) dana bada misali da Hadari, idan mun duba zamu ga cewa hadari yana iya fitowa ba tare da ruwa ya sauka ba. Kaga ya sanar damu abu tun kafin ya faru(Ma'ana dai Leading indicator ne).
Fatan An fahimci wanan!?
Bari mu cigaba...
Bazai yiwu ace wai indicator Kala ɗaya kawai zaka ce ai kai da ita zaka dinga Trading a koda yaushe!!!
Saboda me?
Saboda yanayin kasuwa juyawa yake a koda yaushe, Daga "UP-TREND," ta shiga "Consolidation", zuwa "DOWN TREND,"....
Kasuwa tana iya kasan cewa a Up-trend na tsawon lokaci, Amman Ka saka a ranka fa, wataran dole sai kasuwar juya.
To yanzu Misali:
Mu ɗauki BOLLINGER BAND (BB) ita wannan indicator ɗin ana Trading ɗinta ne idan kasuwa tana CONSOLIDATING/RANGING.
Tana da bangarori guda 3:
1. Upper BAND.
2. Middle BAND.
3. Lower BAND.
Yadda zakayi Trading ɗinta shine: zaka jira farashi ya zo Lower BAND, Sai ka siya. Idan ya koma Upper BAND Middle BAND Sai ka siyar, ka fita daga kasuwar.
So kaga kenan idan har kasuwa tana tashi ne kaje ka kunna BOLLINGER BAND, zai zamana zaka dinga: TRADING AGAINST THE TRADE(Ma'ana kasuwa tana sauka kai kuma yin ƙurin siya). Tunda ita tana aiki ne idan kasuwa tana Consolidating.
Kaga idan kasuwa tana tashi ne, Akwai Indicator daya kamata kayi Amfani da ita, Misali mu ɗauki Moving average(SMA/EMA). ko kuma MACD(Moving average convergence divergences).
Kaga Moving average ana iya Amfani da ita wajan fahimtar daɗewar wannan Trend ɗin:
1. LONG TERM BULLISH/BEARISH TREND.
2. MEDIUM TERM BULLISH/BEARISH TREND.
3. SHORT TERM BULLISH/BEARISH TREND.
Sannan kuma zaka iya Amfani a ita (moving average) A matsayin support ko resistance. Da sauransu.
Haka ma kuma MACD itama kana Amfani da ita ne idan kasuwar tana Up-trend, Domin kuwa ita Lagging indicator ce, sai Abu ya faru take faɗa mana.
A bangaren MACD zamu iya kallo DIVERGENCE, Duk da cewa RSI shine best indicator da nake yin Amfani da ita wajan Fahimtar DIVERGENCE.
Sannan kuma zamu iya trading HISTOGRAM, ko ZERO CROSSES. Duka wannan a ƙarƙashin MACD.
A wasu lokutan muna Amfani da wannan indicators ɗin ne kawai wajan samum ƙarin tabbaci akan wannan zanen da kayi a price Action. Ka tabbatar bakayi kuskure ba, Domin Investors suna iya manipulating Price, Amman idan kayi Amfani da Indicator. Yana matuƙar wuya ayi manipulating ɗinka.
Shawarar da zan baku itace, ku fahimci tsarin Trading ɗinku, sai ku ɗauki indicators da suka dace da wannan tsarin, ka dinga Trading dasu.
Karka ce zaka kunna ko wace indicator, domin hakan zai lalata maka tsarin ka gaba ɗaya.
Hakan zai taimaka maka matuƙa wajan Making faster decisions, which will make your trading process much more efficient.
Allah ya bamu nassara A abun da muka sa gaba!!
Thanks
Menene Cryptocurrency???
MAI TAMBAYA: MENENE CRYPTOCURRENCY...?
AMSA: Ka ƙaddara a ranka crypto wani kuɗi ne na intanet, kamar dai yadda kuɗin takadda yake, sai dai kawai shi banbancinci da kuɗin takadda shine shi a intanet yake. A maimakon kuɗin takadda da gwamnatin ƙasa ke da iko dashi, to shi crypto yana aiki ne akan wani tsarin intanet mai ƴanci wadda ake kira da "Blockchain".
Akan wannan tsarin intanet ɗin na Blockchain ake ajiye bayanan komai na kuɗin crypto, duk wanda ka turawa kuɗin crypto konya turo maka idan aka duba zaayga wannan bayanan akan intanet na Blockchain. Tsarin intanet na Blockchain yana da tsananin tsaro fiye da normal intanet da muke dashi.
Banbancin tsarin Intanet na Blockchain da kuma Normal Intanet da muke amfani dashi shine: Misali kamar facebook yana kan normal intanet da muke amfani dashi, dan haka duk wanda yake amfani da facebook toh facebook suna da cikakken iko dashi.
Toh da ace facebook akan tsarin intanet na Blockchain yake toh facebook basu da wani iko dakai. Wannan dalilin yasa ake wa tsarin intanet na Blockchain laƙabi da "Intanet Mai Ƴanci", kana da damar yin komai naka ba tare da tsangwama ba.
"Idan nace iko ina nufin: Facebook nada ikon rufe ma account naka, restriction dinsa, hanaka comments dss"
Toh su wannan kuɗin crypto ɗin akan tsarin intanet na Blockchain aka gina su, shiyasa suma ake musu laƙabi da "Kuɗi Masu Ƴanci". A maimakon yanzu idan kana da kuɗi a bankinka, toh bankin nada iko dakai, toh su kuɗin crypto idan ka mallake su ka mallaka kenan ba wanda ya isa dasu in ba kai ba.
MAI TAMBAYA: TAYAYA KUƊIN CRYPTO SUKA ZAMA KUƊI DA HAR KAKE IYA CHANZA SU KA KARƁI NAIRA....?
AMSA: Kana ji yanzu idan na kirkiri kuɗin crypto akan Blockchain, da farko zan fara bashi adadi. Misali na kirkiri coin ɗin mai suna $ORC, dana tashi kirkirar sa sai na kirkiri guda 1Million. Toh da farkon lokaci dana kirkiri sa ba komai bane shi illa numbobi.
Lokacin da nake so ya zama kuɗi akwai hanyoyi guda 3 zuwa 5 da ake bi ya zama kuɗi, na 5 ɗin shine wanda yafi rikitarwa:
1. Na farko akwai abinda ake cewa ICO (Initial Coin Offering) ko kuma ace IPO (Initial Public Offering). Shi yadda tsarin yake shine: Zan dauki wannan coin ɗin nawa dana kirkira guda 1million mai suna $ORC, sai na bawa jama'ar gari dama akan su zo su sayi coin ɗin. Wannan kuɗin da zasuyi amfani dashi gurin siyan coin ɗin, shine kuɗin da zai zama abinda ake kira Liquidity.
"Liquidity: kowanne kuɗin crypto na buƙatar shi, Liquidity shine yake baka damar idan kana da kuɗin crypto ka iya chanza shi a baka Dollar ko Naira. Toh wannan kuɗin da ake karba na ICO shi ake amfani dashi guri Liquidity"
MAI TAMBAYA: TOH DAN ALLAH KAFIN KA TAFI NA 2, INA SON KA FAƊA MINI SU WAƊANDA SUKA SAYI COIN ƊIN A "ICO" TAYAYA SUKE CIN RIBA, KO KAWAI SAKAWA SUKE SHIKENAN KUƊIN SU YA TAFI A WOFI..?
AMSA: Shi kuɗin crypto yana hawa da sauka ne, misali idan na sayi coin a ICO yana kan a ƙaddara ₦10, to yayin daya shigo kasuwa mutane suka fara siye da siyarwa dashi. Farashin sa zai iya tashi ya zama ₦50, kaga kenan naci riba ko.
2. Bayan ICO, abu na biyu akwai abinda muke kira da IEO "Initial Exchange Offering", shima dai kamar ICO yake. Sai dai shi a maimakon zuwa da zakayi ka sayi coin direct ta hannun masu coin ɗin, shi IEO a kasuwannin crypto akeyin sa irin su Binance, Kucoin, CoinEx, Bitget dss.
3. Akwai kuma IDO "Initial Dex Offering".
"A crypto akwai tsarin gurin siyayya guda biyu, na farko akwai CEX "Centralized Exchanges" su gurin siyayya ne na crypto da suke aiki kamar banki, sai kayi KYC kayi komai kafin ka fara amfani dasu. Akwai kuma DEX "Decentralized Exchanges" asalin tsarin crypto kenan, shi kuma ba abinda ake buƙata kawai budewa zakayi ka fara amfani dasu"
Toh IDO anayin sa ne a gurin musayar crypto na DEX, shima duk yana aiki ne irin yadda ICO da IEO suke.
4. Sai kuma IFO "Initial Farming Offering", shi kuma sani tsari ne da akeyi wanda za'a ce ka sayi wani coin da tuntuni yana kasuwar crypto ka ajiye sa, za'a dinga baka wannan sabon coin ɗin da bai shigo kasuwa ba kyauta.
5. Sai na ƙarshe sanda yafi kowanne ruɗarwa shine IAO "Initial Airdrop Offering". Shi kuma coin ɗin ake rabawa kyauta ga mutane, amma fa dabara ce da ake amfani da ita dan tara mutane. Misalin irin wannan tsarin, akwai mining da mukeyi.
Suna dabara su tara mutane ta hanyar alkawarin zasu basu coin ɗin su kyauta, sai su ce musu suyi wani aiki. Lokacin da wa'adi ya cika, dama a chan gefe guda akwai wasu manya masu kuɗin crypto da kasuwanni da zasu ga. Ai project kaza yana da mutane da yawa.
Dan haka sai su dauki kudinsu su saka a matsayin Liquidity a sa coin ɗin a kasuwa, su kuma sai a basu wani adadi na coin ɗin, misali coin ɗin guda miliyan daya ne, sai a basu dubu 500k. Sai ace to a hankula zuwa wani lokaci zasu siyar da coin ɗin da aka basu.
MAI TAMBAYA: TOH SU TAYAYA AKE SUKE MAYAR DA WANNAN MAHAUKATAN KUƊAƊEN DA SUKE SAWA AKE BAWA MUTANE FREE...?
AMSA: Na faɗa muku cewa kuɗin crypto hawa yake da sauka ko? Toh mutane sune suke zama sanadin hawan nan nashi da sauka, yayi da suka dinga siya toh farashi zai tashi yayin da sukayi ta siyarwa toh farashi zai sauka.
Toh karka manta coin ɗin da akayi mining dole yana da mutane bila'adadin da suka san shi, dan haka akwai mutanen da muke kira da Traders da kuma Holders a crypto. Da zarar sun samu labarin coin ɗin zasu fara saka kuɗi, hakan zai sa ya dinga tashi.
Ta yiwu an saka shi a ₦100 duk guda daya, toh bayan Traders da Holders sun fara siya sai kaji farashin ya dawo ₦800. Su kuma wannan manyan masu kuɗin crypto da kasuwannin dama an basu guda dubu 500k, kamar yadda aka musu alkawari.
Sune suka saka masa kuɗi ya fito a farashin ₦100, kaga kenan idan suka siya a ₦100, sai dai ma su faɗi basu ci riba ba. Amma da sun tsaya yaje farashin ₦800, toh yanzu ya ninka musu kuɗin su x7. Kaga suna cikin riba.
Akwai coins da yawa a kasuwar crypto, yanzu haka akwai guda sama da dubu 30k. Dan haka babban abinda kowanne project na crypto suke nema shine a sansu, ba kuma za'a san su ba sai mutane sun san su. Hakane yasa suke neman mutane suyi mining ko task.
Yin wannan mining ɗin da task ne yake sawa duniyar crypto ta san project din, tunda maybe dubbunai ko miliyoyin mutane ke mining ɗin ko task. Dan haka da zarar ya fito, Traders da Holders na crypto suke fara siyansa. Wannan ke sawa farashin sa ya tashi.
Wallahu Ya'alamu....!
#eth overview
Ethereum (ETH) is the second-largest cryptocurrency by market cap and plays a foundational role in the blockchain ecosystem. Here’s a breakdown of its current position and future outlook:
---
1. What Makes Ethereum Important
Smart Contracts: Ethereum pioneered programmable contracts, enabling decentralized apps (dApps), DeFi, NFTs, and DAOs.
Ecosystem Leader: Most altcoins and tokens are launched using Ethereum’s ERC-20 or ERC-721 standards.
Proof of Stake: Since "The Merge" (September 2022), Ethereum uses Proof of Stake (PoS), making it more energy-efficient and scalable.
---
2. Ethereum in 2025
Price (Current Range): ETH has hovered between $2,800 – $3,500 in early 2025.
Bullish Targets: $5,000 – $10,000 is possible by late 2025 if scaling solutions succeed and institutional adoption rises.
Catalysts:
Layer 2 growth (Arbitrum, Optimism, zkSync)
Institutional DeFi and ETFs
Real-world tokenization (e.g., real estate, stocks)
---
3. Challenges
High Gas Fees: Still an issue during network congestion, though mitigated by Layer 2s.
Competition: Solana, Avalanche, and other chains are faster and cheaper.
Regulation: SEC scrutiny could affect ETH’s status as a commodity or security.
---
4. Use Cases Growing in 2025
DeFi (Decentralized Finance)
NFTs and gaming
DAOs (Decentralized Autonomous Organizations)
Tokenized real-world assets
Stablecoin infrastructure (USDC, DAI on Ethereum)
$ETH
"Bayani a taƙaice game da ID/USDT "
Farashin ID yana kan $ID 0.2432 (+8.19% a cikin sa’o’i 24), yana nuna karuwar sha’awa da saye daga masu saka jari. An ga ƙarancin farashi a $0.1806 kwanan nan, amma yanzu yana ci gaba da hawa. Moving Averages (MA5, MA10, MA20) duk suna goyon bayan ci gaba, wanda ke nuna bullish trend.
Karin Magana Hausa
“Idan jini ya hau rago, to barasa ce ta motsa shi.”
Ma’ana: Idan farashin coin ya fara hauhawa da ƙarfi, akwai wani abu da ke motsa kasuwa – ko dai labari, ko gagarumar saye.
Shawara: Idan kana cikin ciniki, ka tabbatar da saka stop loss don rage hadari, domin kowane hauhawa yana iya biyo da sauka.
#Maher Abdullahi crypto hausa#
Bitcoin: No Magic, Just Mathematics – The Engineering Behind the $100K Phenomenon
Bitcoin’s meteoric rise to over $100,000 may seem like digital alchemy — a financial miracle born out of thin air.
But as Axel Adler Jr., Verified Author at CryptoQuant, reminds us, Bitcoin is no cosmic accident. It is the culmination of decades of cryptographic development and economic design — an engineering masterpiece, not a mystery.
Building Blocks from the PastLong before Satoshi Nakamoto published the now-famous Bitcoin whitepaper in 2008, the technical foundation was already being laid:
Merkle Trees (1979): Introduced the structure for efficiently verifying data.
Hashcash (1997, Adam Back): A proof-of-work system originally designed to fight email spam.
b-money (1998, Wei Dai): An early vision of anonymous, distributed money.
Bit Gold (2005, Nick Szabo): A direct precursor to Bitcoin’s value proposition.
Satoshi didn’t invent Bitcoin out of a vacuum — he synthesized these innovations into a single, functional protocol. As Adler puts it, “Simple rules — complex behavior.”
Two Lines That Changed Finance
Bitcoin’s brilliance lies in its simplicity:
Block reward halves every 210,000 blocks (roughly 4 years)
Maximum supply capped at 21 million coins
This predictable, transparent issuance model introduced a new monetary paradigm — one where scarcity is enforced by code, not central banks.The Four-Year Cycle: Pattern or Projection?
Adler emphasizes that the now-famous “Bitcoin four-year cycle” — often tied to halving events — is more structural than mystical. The halving aligns neatly with macroeconomic timelines like U.S. presidential elections and central bank policy shifts. But he cautions against over-romanticizing the past:
“What looks like fractal magic today is often just a trick with mirrors called ex-post curve-fitting.”
We see repeating patterns not because they’re ordained, but because human minds and markets respond predictably to the same constraints — scarcity, fear, greed.No Aliens, Just Code
Dispelling the aura of mystery, Adler writes: “No aliens. No time machine. No magic.” Just a few lines of code from a possibly small group of skilled developers — and a transparent monetary policy that continues to shake global finance to its core.
As Bitcoin marches through another halving cycle, and the market digests both its predictability and its potential, it’s important to remember: the future isn’t being conjured — it’s being engineered.$BTC
Dai社群媒體數據
過去 24 小時,Dai社群媒體情緒分數是 4,社群媒體上對Dai價格走勢偏向 看漲。Dai社群媒體得分是 2,012,在所有加密貨幣中排名第 152。
根據 LunarCrush 統計,過去 24 小時,社群媒體共提及加密貨幣 1,058,120 次,其中Dai被提及次數佔比 0.01%,在所有加密貨幣中排名第 227。
過去 24 小時,共有 63 個獨立用戶談論了Dai,總共提及Dai 108 次,然而,與前一天相比,獨立用戶數 減少 了 7%,總提及次數減少。
Twitter 上,過去 24 小時共有 3 篇推文提及Dai,其中 100% 看漲Dai,0% 篇推文看跌Dai,而 0% 則對Dai保持中立。
在 Reddit 上,最近 24 小時共有 0 篇貼文提到了Dai,相比之前 24 小時總提及次數 減少 了 100%。
社群媒體資訊概況
4